KOMAI TSANANI
KOMAI TSANANI
By Pharveenahwrites
Alhamdulillah ya rabbi yadda zan fara littafinnan ka nuna mana mungama lpy
Chapter 1
Gefen rafi wasu yan mata ne guda hudu biyu a gefe biyu kuma suna diban ruwa cen daya daga cikin yan matan da suke a gefe tace Wai binto ba zakuba manyan ku waje su diba Ruwan ba banda munafurci ba abunda kuke shegiya mata uba wacce aka kira da binto ce tace aunty bibalo ynx zamu tashi tülün haule ne ya fashe yarinyar da aka kira bintalo yarinya ce da bazata wuce shekara 14 a duniya ba ita ba fara ba ita ba nawa ba haka suka dauka tulun binto ita kuma haule nata ya fashe suka bi hanyar da zata kaisu gida suna tafiya haule ke cewa binto ke ynx haka zaki zauna bibalo tana zagin ki kamar ba gida daya kuke ba tace Haba haule kidena fadin haka zagin da tayimun Akan bamu basu waje bane Kinga su manyan mu ne Sai haule tace ke kikaji zaki iya tunda bada ma ayi magana kan laifin da ake maki Kinga tafiyata ta tafi barta a baya koda haule ta wuce binto Cewa tayi haule bazaki gane mgnta ba Sai wata rana.
A wani katafaren gate fari kal motoci guda uku baqaqe qirar benz suka tsaya inda motar gaba tayi horn mai gadi ya bude duka suka shigo motar tsakiya ce daya daga cikin guards din motar baya aka bude Wanda ke ciki ko leqe baiyi ba bare fitowa andauka kusan minti 2 tukun ya fito fari ne taş yasa glass baki kayan jikin shi kadai zasu tabbatar maka da soja ne Sbd Kayan sojoji ne jikin shi yana waya cen yace John i will call u just arrived now ya yanke kiran ya kalla gidan yace Alhamdulillah finally am home cen Gaban sa yafadi bayan yatuna wacce zai isko gidan Duk duniya ko mahaifiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron umma,umma ta kasance idan baya gidan ko tuna ta bayason yi Sbd abunda idan tace zaayi to tabbas Sai anyi shi kuma shi har ynx kallon yaro yakema kansa ya kasance irin mazan nan ne jikin su kawai abun kallo ne kakkarfa ne ba na wasa ba Dan kallo daya zakiji tsoron sa amma umma ta kasance wacce ke wasa da zuciya da kwakwalwarsa yadda taso
Duk mai son cigaban ya rubuta mana NEXT a comment
KOMAI TSANANI* (Maganin shi Allah)🤲✍️
Bismillahir rahmanir raheem
Dafatan kowa yana lpy yan uwana musulmai mu riqe istigfari da azkhar ya kasance abun yin mu akoda yaushe duniya ta sauya ynx Allah ne kawai zai tsaremu Allah ya taimaka
*Page* 2
Yafi 5mins yanaso yashiga gidan amma ya kasa shiga cen dai yace bari ya shiga kafin shigar shi ma Sai ga kannenshi mata guda biyu da sukazo tarban yayan nasu yakallesu kyawawa ne sosai farare kalar fatarshi shima koda suka karaso gun suka hade bakin wajen fada u are welcome big bhai ya hanya yace Lpyqlau summy and surry Dafatan kuna lpy sukace Lpyqlau ya umma fa da Ammie summy tace Ammie ce kawai a gidan amma umma ta tafi gidan addan ta wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yake mutafi ciki 🚶🚶♀️🚶♂️
Binto ce ta shiga gidan su da kallo daya zakasan gidan talakawa ne tayi sallama Wata mata ce zaune kan kujera tana dama kunu ta dago ta kalleta a masife dace Dan ubanki Sai ynx zaki kawo mun Ruwan tau ga Uban riqonki cen Sai Kije ki wankeshi da Ruwan binto dai yarinya ce karama amma akwai kaifin basira fa hankali ta juya inda ake zuba Ruwan ta zuba Sai ta kalla inda kawu ke kwance tace kawu ina wuni ya jiki yace Lpyqlau fatima Sannu Allah yayi maki albarka ya jikan mahaifiyar ki ya sadaki da Mahaifinki tace ameen,inna meramu ce ke fadin zakizo na aike ki ko Sai jikinki ya fadamaki a sanyaye ta tashi tace inna gani Kije gidan malka Kice tabani sako kuma kiyi Sauri saura ki tsaya magana da yan gari tace tau inna ta fita daga gidan a sanyaye ita dai Batasan me tayi ma umma ba kullum kamar haushin ta takeyi😡
Koda ya shiga shiga tare da kannensa sumayya da Surayya path din Ammien su suka shiga tana kan sallaya da alama sallah ta idar ta daga kai da kalleshi tace saukar kenan eh Ammie Alhamdulillah Dafatan na sameku lpy tace Lpyqlau ya gajiya yace Alhamdulillah tace tau kaje ka samu kayi wanka ka huta ku kuma kuje daya ta hadamai tea daya Ruwan wanka yace aa Ammie su hada tea din zanyi na Ruwan wankan ta gyada kai ya wuce path dinshi gidan path hudu ne path din Abban su,Ammie,da Umma Sai nashi yana shiga path dinshi yaga komai yadda yabarsa yace Alhamdulillah gida dai gida ne Duk Wanda yabar gida ya barshi ya shiga bedroom Dan yasamu cire kaya yashiga bathroom 🚽 domin wanka
Sallama tayi a gidan yafi gidan su tsufa Sai da ta sakeyi aka amsa tace ina wuni inna malka a yatsine tace lpy😒Sai binto tace dama innanmu ce tace nazo karbar sako bude bakin malka tace innar bibalo dai ke banda abun ki ina Shege da gidan yan halal batace komai ba ta sunkuyar da kai kasa cen ta dauko bokiti fari tace karba ki kaimata Kice adawomun da bokiti na tace tau Sai anjima malka tace ajima dayawa dangin tsiya uwa tazo ta kawoki Wai ariqa amana ba uba tayi tsaki da koma daki😏
Tapiya take a hankali Sai ga yara sunzo suna a su shegu ina zuwa? Bata tankasu ba su ka hau dariya😂🤣Sai daya daga cikinsu tace meye a bokitinnan tace Duk abunda zakuyi kuyi iya kaina Banda bokitinnan Sai sukace ai kuwa Sai mungani nan akahau rigimar karbar bokitinnan ai kuwa yafadi abun ciki ya zube a kasa daura hannu tayi aka ta fashe da kuka tana fadin yau ni binto na shiga uku yau inna Saita kasheni Innalillahi ta fashe da kuka😭😭😭😭
Boko by pharveenahwrites
Idan littafinnan yayi dadi kunason cigaba ku rubuta NEXT a comment kuma ku ziyarci
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7E7ew4SpkLSi0Slo2D
pharveenahwrites.blogspot.com
KOMAI TSANANI*(Maganin shi Allah)🥹🤲🙏
Da sunan Allah mai rahama mai Jin kai Allah yasadamu da alkhairan cikin wannan rana Ameen🤲
*Page* 3
Kuka take sosai amma yarannan dariya suke😂daya ta zuba a guje ta yi hanyar gidan su binto tana kaiwa tana haki take cewa inna meramu yau binto ta afka maki aika aika fada take tokala Sai sakon ki ya zube a kasa Gatacen tana cewa Wai Duk abunda zakiyi saidai kiyi ai inna meramu batayi wata ba ta antayo Ashariya tace yau mai Hana naci Uban binto a gidannan Duk da bata dashi Sai Allah ke mutafi ta saka hijab dinta yasha duniya may be tun 199 tintini yake😂😁😝🤪
Bayan ya rage Kayan jikin shi ya dau towel ya nufa bandaki ya hada ruwa yadda zasuyi kasa ya fara wanka cen yakejin wayar sa tana ringing anata kira tsaki yayi yace ko Waye wannan ke kira na kamar na saci kidney din shi 😒fitowarsa kenan aka sake kira Sai yaga leemah😡 haka yasa a saving ya dauka yace i just arrived pls call me later ya yanke kiran ba tare da Jin ko salllamar da tayi ba a bangaren leemah kuma hawaye ne take tana fadin gsky dole nayi magana da umma Akan bawan Allahn nan ko Dan Inason sa yake wulaqantani (lol 😂 halin maza ne baki sani ba sis leemah)
Tafiya inna meramu keyi kamar zata tashi sama isowarta gun ta dauke binto da lpyayyun Mari biyu tace Dan ubanki Kinsan nawa ne kika zubar aa uwar ki ma yakamata ai tunda ba Uban yau Sai na miki dukan ajali( yah Subhanallah Ana dukan ajali ne jamaa) ta ja hannun ta suka tafi yarannnan kuwa dariya suka saka Kinga ai ynx mun nuna mata mu munada uwa kuma munada uba mu ba shegu bane😂😂😂
Ya shirya tsab acikin kananan kaya na Shan iska Sai ga surry dauke da mug na black tea Sai kamshi yakeyi tayi sallama tace big bhai ya gajiya ba annuri ko wasa yace Alhamdulillah tace idan ka gama Umma ta dawo take Gaban sa yayi mummunan faduwa yace yah Subhanallah Astagfirullah Al-Azeem Sbd ya samu nutsuwar zuciya kasa Shan t black tea din yayi yanata maimaita astagfirullah-Al azeem har yasamu nutsuwa Sai ya dau tea din yakai baki Sai ga kira ya shigo wayar sa ganin mai kiran ya sa Gaban sa sake faduwa🥹
Me wannan umma takeyi ne da big bhai namiji cikakke ke tsoronta ku biyo mu zaku samu amsar
pharveenahwrites.blogspot.com https://whatsapp.com/channel/0029Vb7E7ew4SpkLSi0Slo2D
✍️✍️Page 4📑✍️
Lokacin da inna meramu suka isa gida tun a bakin gida take dukan binto kamar wacce aka aiko ta jibgeta kawai tace Allah bai wulaqanta meramum baba ba babu wata shegiya da aka kawo da zata wulaqantata ynx Kinsan kudina da nasa akan abunda kika zubar binto kuka take Kamar ranta zaifita kawai Sai ga bibalo da take gun diban ruwa a rafi Sai ynx tadawo wa gidan tace innanmu lpy waccen shegiyar ce mana ta zubar da sakon da na fadamaki gun malka ai kuwa bibalo ta sauke tulun Ruwan ta ta zabgawa binto Mari tace yar hassada da bakin ciki ta Allah bai taki ba Sai na auru a gidannan baba ma da yake tare ki yafita innanmu ki bani abun duka Dan Allah inna meramu dai tace aa bibalo ki barta ai ko ynx Jikinta ya gayamata maza tashi Kije kimin wanke wanke banza yar Tasha ba uba (yah rabbi ka rabamu da maraici 🥹🤲)
Black tea dinshi yake sipping amma ji yake duka ya rasa appetite🤢 wayar sa ce take sake ringing a karo na uku ya dauka wata murya ce da bazaka tantance yana yinta ba tayi magana cewa baa fadama na dawowa gidan bane yace umma Ganinan zuwa kaya nake canjawa ta yanke kira jiki a sanyaye ya mike ya dauka wayar sa qirar iPhone 📲 ya fita
Direct dakinta ya nufa ya Nashiga yayi sallama ta amma mace ce iya mace hajiyoyi masu ji da naira ta kalleshi tace bismillah zauna zama yayi a kasa tare da fadin umma ina wuni ya gdn ya muka sameku saukata naji kinfita unguwa kallonsa tayi kadaran kafaham tace lpy Wato Sbd kar nayi maganar da na Saba ne yasa ka qin zuwa bayan kaji na dawo ko yace aa umma ina wanka ne tay Masha Allah kaje kaga leemah idan kadawo zamuyi magana yace shikenan umma zanje ya miqe ya nufa kofa yana fita Zuciyar sa tafara zafi ya rasa Meyasa tsoron umma aransa yafi na mahaifiyar da ta haifeshi 🫥
Wanke wanke binto takeyi tana kuka ga ciwon kai da yunwa Duk sun sake saka mata wani ciwon tagama tafara Shara kenan bibalo ta sake zubar da wani sharan ta dago ta kalleta kwata kwata bibalo bazata fi shekara 16 ba girnman Jikinta kuma zaisa ka dauka tayi 19-20 tace wa kike kallo mara kunya ta duqar da kai bibalo tace ohhh ga yar iska ina magana kin shareni ta camuko ta ta wanke fuskar binto da Mari a take wajen ta zube kasa ba numfashi yayi daidai da shigowar kawu kuma Mahaifi ga bintalo😧😳😱
Muhadu a page 5 in Allah ya kaimu
Mezaifaru ga baban bibalo ya shigo gidan binto ta fadi? Wacece binto ? Ina Mahaifanta Duk zaku samu amsar wannan idan kuma tare damu ku biyo mu Domin samun cikkakiyar amsa 🤗
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7E7ew4SpkLSi0Slo2D. pharveenahwrites.blogspot.com
KOMAI TSANANI (Maganin shi Allah)🥹🤲
Brk da warhaka mutanen arziki Dafatan kowa yana lpy Allah ya sadamu da alkahiran wannan rana Allah yayi mana mafita ta alkhairi
Page 5
Kawu ne baban bibalo yashigo da hanzari yayi gun binto da take kwance a kasa ya ce bibalo zaki ban ruwa ne ko Sai na tashi na rama marin da kika mata Jikinta na rawa ta bashi Ruwan tana cewa yau baba ne da dakaman tsawa Akan yar da batada Uba 😒yayyafa ma binto ruwa yayi taja numfashi tare da fadi aunty bibalo kiyi hakuri Dan Allah ban Harare ki ba 🥹tana kuka kawu ne ya kamata ta jingina da gini ya bata ruwa tasha yace binto kiyi hkr in sha Allah Allah yana tare dake 🤲
Tafiya yake acikin motar kamar bayaso haka kawai jikin shi ya mutu shidai bazaice bayason leemah ba amma kwata kwata bayajinta aranshi biyayya wa umma ce kawai tasa zaije ganinta,motar shi yayi parking a daidai wani gate madaidaici ya dauka waya ya danna kira kamar jira take ta dauka am outside kawai naji ya fada,bayan kamar mins 3 Sai ga leemah yar kyakkawa ta sa doguwar abaya da sunne kai ta gaisheshi tace mu shiga ciki ko? Aa umma ce tace nazo naganki Ykk ya gida ?lpy qlau ya hanya Alhamdulillah tau ni zan wuce ga sako ya bata leda bai jira wani Abu ba yaja mota a 30 😂 yabar layin (hummm anya wannan lpy yake kuwa haka ake Fira😂)
Dawowar inna a gidan yasake haddasa masifa Dan kuwa bibalo ta kwashe karya da gsky tafadi Cewa tayi ma binto ce tafara marinta ai kuwa inba tace Banga yar da aka Haifa ba uba ba da zata dakar man ya gidannan shi kuma kenan ina tufka ana kuncewa kenan dole nayi sabon aiki(ya Subhanallah Allah kasa mudace) dakin da binto da bibalo ke bacci ta nufa tana shiga tahau dukan binto wacce suman ne kawai bata kumayi ba bayan tasha duka ta fito tace umman mu kiyi hakuri bazan sake ba aunty bibalo kema kiyi hkr dan Allah🙏inna tace ai indai ba gidannan bakyanan ko kinmutu ba babu abunda zai Hana nayi miki dukan mutuwa akan ya ta Kije madafa kanzon shinkafa na kife a kwano kici babu mai kisa goshiri ngd sosai inna kawai ta fada ta miqe🥹
Dawowarsa gida part din mahaifiyarsa yaje ko ya ji sanyi a ransa yana shiga taga yanayin shi tace lpy yace ba komai Ammie zauna dama Inason fada ma ranar Monday zamuje health talks a wani kauye nan kusa Wai MADA a samu addua yace Ammie Allah ya taimaka Abba ma ya kirani yace yana hanya tace Sai kafadawa umman ku Dan saukarta ne atake yaji zufa kuma Gaban sa ya fadi yace shikenan Ammie bari naje,badamuwa Allah yataimaka Ameen Ammie😍🙏
Ya shiga part din umma ance tana bathroom yace afadamata Abba yana hanya Sai Yawuce nashi part din ya rage Kayan jikinsa ya kunna AÇ ya zauna tare da jawo laptop dinshi zai fara aiki
Cin Kanzon nan Dan yazama dole gareta ne yasa takecin shi da ruwa taji sallamar kawu ta amsa,inna kamar jira take tafara masifa ita dai binto shiru tayi kanta yana juyawa tun tanajin hayaniyar inna har takai dif bata gani bataji gabadaya ta zube a kasa 🥹😞
Meyake damun binto ne da ta sake suma? Idan Abban su big bhai yadawo mezaifaru? Wacece Ammie ya zamantakewar ta da umma yake a gidan? Duk zaku samu amsar idan kuna bibiyarmu kuyi like share da comment Domin samun cigaba
pharveenahwrites.blogspot.com
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7E7ew4SpkLSi0Slo2D
Comments